Ƙilu Ta Ja Bau! Jami’an Tsaron Farin Kaya Sun Cafke Wani Ɗalibi Kan Aisha Buhari

Alfijr ta rawaito Wani dalibi dan shekara 23 a jami’ar tarayya Dutse ya shiga hannun jami’an tsaro na farin kaya (SSS) bisa wani rubutu da ya wallafa a dandalin sada zumunta na yanar gizo da ta ke ganin ya bata sunan mai dakin shugaban ƙasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari.

A cewar rahotanni, Aminu Adamu Muhammed a watan Yunin 2022, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ba zato ba tsammani Misis Buhari ta kara nauyi sosai bayan da ta taka rawar gani wajen wawushe dukiyar kasa yayin da talakawa suke shan wahala a karkashin mulkin mijinta.

Muhammed ya kira Aisha Buhari da cewa “Su mama anchi kudin talkawa ankoshi”, wato ta yi kiba ta hanyar cin kudin talakawa.”

A nasu bangaren abokan Muhammad sun ce ya yi wannan karambanin ne saboda ya ji takaicin yajin aikin da jami’o’in kasar suka dade suna yi.

Sai dai a nasa bangaren ya musanta dukkan ikirarin.

Wata majiya daga danginsa, ta ce jami’an ta sun dauke Muhammed ne a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022, a harabar jami’ar tarayya dake Dutse, Jigawa.

A takaice dai an wuce da shi Abuja, an kuma ba shi izinin tuntubar mahaifinsa Adamu Shalele Azare, game da inda yake, wanda ‘yan uwa suka dauka ofishin ‘yan sanda ne.

Daga baya an bayyana cewa hukumar tsaro ta jihar ce ke da hannu a kamun Muhammad.

Hukumomin makaranta, ciki har da sashen fasahar muhalli inda Muhammed ke karatu, sun ki cewa komai game da lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *