Alfijr
An gano dan Pantami da aka yi garkuwa da shi a Bauchi Ali Isah Ali, dan shekara 14
Alfijr ta rawaito dan Ministan , wanda aka yi garkuwa da shi da yammacin ranar Alhamis a Bauchi ya Shaki iskar yanci.
An sace Ali jim kadan bayan rufe makarantar Islamiyyarsu, a ranar Alhamis da yamma, yaron dalibin JSS 2 ne a makaranta mai zaman kanta, inda mahara sun zo ne akan babur
Mahaifiyar Ali a cikin sakon da ta aika ta WhatsApp din PTA na makarantar ta tabbatar da sace shi.
Alfijr
Sakon wanda aka tura da karfe 10:29 na daren ranar Alhamis ya ce; “An sace dana, don Allah ku sa shi cikin addu’o’in ku.
Daga baya an gano yaron a wani wuri da ke kan titin Dambam.
A wata tattaunawa ta wayar tarho mahaifiyar Ali ta ce an same shi a wani shingen bincike kuma yana gida yanzu haka cikin koshin lafiya., in ji ta.
Alfijr
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce suna kan aikin.
Kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta wallafa