An Kaddamar Da Kuɗin Ingila Mai Hoton Sarki Charles

Alfijr ta rawaito Babban bankin Ingila ya fitar da sabbin takardun kudi masu dauke da hoton Sarki Charles.

Hoton Sarkin zai fito ne a takardun kudi na fam biyar da 10 da 20 da kuma 50.

Bankin ya ce kudin za su fara shiga hannun mutane a tsakiyar shekara ta 2024.

Za a ga hoton Sarkin a gaban jikin kudin da kuma idan an daga su ta gefen alamar tsaron jikin kudin.

Bankin ya ce za a ci gaba da karbar tsoffin kudin kasar a shaguna koda an fara amfani da sabbin masu dauke da hoton Sarki Charles.

Sarauniya Elizebeth, ita ce basarakiya ta farko da aka sanya hotonta a jikin takardun kudin Ingila wanda aka fara a 1960.

BBC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *