Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun tsunduma yajin aiki sakamakon wasu dalilai.
Alfijir labarai ta rawaito Kafin su tsunduma yajin aikin sai da ma’aikatan suka gabatar da yin sallah tare da gudanar da alqunuti don Allah kawo musu dauki sakamakon mawuyacin halin da suke ciki.
Sun dai bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon yadda gwamnati ta Kasa fara biyansu mafi karancin albashi na naira 71,000 da gwamnan Kano ya Amince da shi.
Sun kuma ce bayan kin biyansu mafi karancin albashin, sun akwai ragowar hakkokinsu da suka ce gwamnatin Kano ta gagara biyansu.
Dukkanin kokarin da muka yi na jin ta bakin Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano don jin na su bahasin ya ci tura, Amma za mu cigaba da bibiyar lamarin.

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ