Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin dage taron majalisar zartaswa ta tarayya zuwa wani lokaci, wanda za a sanar nan ba da jimawa ba.
Alfijir labarai ta rawaito tun da farko dai an shirya gudanar da taron ne a yau Laraba amma an dage shi domin girmama babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,wanda ya rasu a daren ranar Talata.
Janar Lagbaja ya rike mukamin babban hafsan soji daga ranar 19 ga watan Yunin 2023, har zuwa rasuwarsa a ranar 5 ga watan Nuwamban 2024.
A jawabinsa, shugaba Tinubu ya ba da umarnin a rage tsawon tutoci na tsawon kwanaki bakwai a fadin kasar domin karrama Janar din da ya rasu.
A safiyar yau ne shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan Lagbaja da rundunar sojojin Najeriya. Ya kuma yi masa addu’a, tare da jinjina irin gudunmawar da ya bai wa al’umma.
‘Yan majalisar zartaswar da suka taru domin taron sun Mike tare da yin shiru na tsawon minti daya domin karrama marigayin.
RN
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇