APC Ta Kuma Shan Kayi A Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya Tare Da Cin Tararsu ₦ 600,000 A Kano

Shari'ar Zabe

Kotun Sauraren KORAFE Korafe-korafen Zabe Ta Kori Karar Da Aminu Goro Da Jam’iyyarsa Suka Shigar Akan Kujerar Majalisar Tarayya A karamar hukumar FAGGE

Alfijir Labarai ta rawaito bayan doguwar muhawara kotun sauraron ƙararrakin ƙorafe ƙorafen zaɓe ta kori ƙarar da tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge Hon. Aminu Sulaiman Goro ya shigar tare da jam’iyyarsa ta APC da suke ƙalubalantar nasarar jam’iyar NNPP tare da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Fagge Hon. Barr. Muhammad Bello Shehu (M.B Shehu Fagge).

Kotun ta tabbatar da nasarar Hon. Barr. M.B Shehu Fagge a matsayin zaɓaɓɓen ɗan majalisa, inda daga bisani ta umarci ɗan takarar jam’iyyar APC da jam’iyyar tasa akan su biya wanda sukai ƙara, jam’iyyar NNPP da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC tarar dubu ɗari shida (600,000) saboda ɓata musu lokaci da sukai, inda za’a rabawa rukunin na mutane uku kowa dubu ɗari biyu, biyu.

Barr M B Shehu Fagge
Barr M B Shehu Fagge

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *