Atiku Abubakar Ya Yi Martani Ga Mataimakin Shugaban Kasa Kan Batun Yi Masa Ritaya

Atiku ba zai iya aminta da ƴan fashin zabe ba saboda yin hakan zai zama fyade ga burin ‘yan Najeriya da suka kwashe shekaru suna fafutukar gwagwarmayar tabbatar da sahihin zaɓe.”

Alfijir Labarai ta rawaito Ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa lokacin ritayarsa a siyasa bai yi ba tukunna

Atiku ya kuma musanta rahotannin cewa ya taya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu a kotun zaɓe

Hakan na zuwa ne a matsayin martani ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya ce zai yi masa ritaya, sannan ya siya masa tumakai da awakai domin ya je yayi kiwo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sha alwashin cigaba da bayar da tashi gudunmawar wajen ganin dimokuraɗiyya ta samun wajen zama a ƙasar nan.

“Ba zai yi ritaya ba a maimakon hakan zai cigaba da kasancewa cikin gwagwarmayar ganin dimokuraɗiyya ta samu wajen zama a ƙasar nan.”

A cewar sanarwa Atiku bai ta ya Tinubu murna kan nasarar da ya samu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ba: “Atiku ba zai iya aminta da ƴan fashin zabe ba saboda yin hakan zai zama fyade ga burin ‘yan Najeriya da suka kwashe shekaru suna fafutukar gwagwarmayar tabbatar da sahihin zaɓe.”

Gaskiya Ta Bayyana “Idan sun gamsu cewa nasarar da suka samu tana da inganci, ina ganin ba buƙatar su tsaya suna yi wa yan adawa zagon ƙasa wajen taya su murna ta hanyar labaran karya.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *