Ba Ministar Jin Ƙai Ce Kaɗai Ta Aikata Almundahanar Kuɗi Ba – In Ji Atiku

FB IMG 1704886903715


Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wasu masu hannu a badaƙalar almundahanar kuɗi da ake zargin ministar jin ƙai, Betta Edu ta aikata.

Alfijir labarai ta rawaito Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jamiyyar adawa ta PDP a Zaben 2023, ya bayyana hakan yayin da yake yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan matakin da ya dauka na dakatar da ministar jin ƙan, duk da a cewarsa hakan ma kaɗai bai wadatar ba.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar, inda kuma ya umarci hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta gudanar da bincike a kanta.

Matakin na zuwa ne bayan ya fuskanci kiraye-kirayen ɗaukar mataki a kanta saboda zarge-zargen tafka almundahana, wanda ministar ta musanta


Ministar da aka dakatar ta fuskanci gagarumar suka ne bayan kwarmata wasu takardun kashe kuɗi daga ma’aikatarta, waɗanda suka nuna ta bayar da umarni ga babbar akanta ta biya naira miliyan 585 cikin wani asusun ajiyar wata, lamarin da ake zargin ya saɓa ƙa’idojin kashe kuɗi na gwamnati.

Aminiya ta ruwaito cewa cikin wata wasiƙar martani da wani mataimakinsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce abin takaici ne ganin yadda shirin da aka kafa da zummar tsamo ’yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci amma kamar yadda ake zargi ya zama saniyar tatsa ga gwamnatocin jam’iyyar APC.

Ya ce, “Ko da yake Tinubu ya cancanci yabo saboda dakatar da Betta Edu, amma muna da yakinin cewa an ɗauki matakin a makare.

“Da farko, ba shi [Tinubu] da wani dalilin wajen naɗa ta a matsayin minista a irin wannan muhimmiyar ma’aikata. Sai dai Tinubu ya fifita siyasa a kan ƙwarewa, lamarin da ya janyo wannan abin kunya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *