Babbar Magana! Zargin Badaƙalar Naira Biliyan 33: Tsohon Ministan Lantarkin Buhari Ya Sume A Kotu

FB IMG 1720710560375

Tsohon Ministan Wutar Lantarki a mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari  Injiniya Saleh Mamman, ya fadi a kotun da ke sauraron shari’ar zargin sa da badakalar kudade.

Injiniya Saleh Mamman ya yanke jika ya fadai ne a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, sakamakon rashin lafiya a kodan da ake gurfanar da shi kan zargin karkaar da Naira bilian 33.

Mamman, wanda aka kai kotun a safiyar Alhamis, ya fadi ne kafin a kira shari’ar.

Alfijir labarai ta rawaito cewa lauyan tsohon ministan, Femi Ate, SAN, ne ya shaida wa Mai Shari’a James Omotosho hakan jim kadan da aka kira shari’ar.

Da aka ci gaba da sauraren karar, tsohon ministan ya shiga akwatin ba da shaida, inda aka ga wani bangare na tufafinsaa jike sharkaf.

Hukumar EFCC ta shigar da karar Mamman tuhume-tuhume 12 na karkatar da kudade da safarar kudaden haram Naira biliyan 33.

A ranar 10 ga Mayu, 2021, aka kama tare da tsare tsohon ministan da ya yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Buhari daga 2019 zuwa 2021, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

A ranar 1 ga Satumba, 2021 ne Buhari ya sallami Saleh Mamman tare da Ministan Noma da Raya Karkara na lokacin, Sabo Nanono a wani abin da ake kira sake fasalin majalisar ministoci.

An zargi Mamman da hada baki da ma’aikatan ma’aikatarsa da ke kula da asusu na ayyukan wutar lantarki na Zungeru da Mambilla don karkatar da kusan Naira biliyan 22.

Binciken ya gano wasu kadarori a Najeriya da kasashen ketare da ake zargin suna da alaka da wadanda ake zargin, yayin da aka ce an kwato miliyoyin Naira da daloli a hannunsa.

NAN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *