Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya sa gwamnatinsa ta ninka kuɗaɗen da take bai wa jihohi daga asusun tarayya sau uku.
Alfijir labarai ta rawaito cewa da yake magana yayin taron shugabannin jam’iyyarsu ta APC a Abuja ranar Talata da dare, Tinubu ya lissafa abubuwan da ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnatinsa damar yi.
“Babu ta yadda za a yi Najeriya ta ɗore matuƙar ba a daina biyan tallafin [man fetur] ba,” in ji shi.
“Mun ninka kaso na kuɗin da jihohi ke samu sau uku. Muna da isassun kuɗin da za mu bai wa ƙananan hukumomi. Mun kafa hukumar Nelfund da za ta dinga biyan kuɗin karatun ‘ya’yanmu.
“Za mu iya saita makomar ƙasar nan. Abubuwan da ke faruwa a duniya na burge ni, ba don komai ba sai yadda suke koya mana darasi cewa mu ‘yan Najeriya za mu iya gina kanmu kuma mu taimaka wa Afirka ta ci gaba.”
Matashiya: Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, wanda ya sa farashinsa ya tashi daga ƙasa da N200 zuwa sama da N1,000 a yanzu.
BBC
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ