Barr, Abba Hikima ya sanar da miƙa jimillar kuɗaɗe miliyan 25 ga Malam Haruna waɗanda aka tattara a matsayin tallafi bayan rasuwar Iyalansa.

FB IMG 1769174372830

Cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Abba Hikima ya bayyana cewa an tattara waɗannan kuɗaɗe ne a cikin asusunsa na banki cikin kwanaki shida kacal da rasuwar.

Ya ƙara da cewa, cikin jimillar kuɗin, akwai Naira miliyan 3.4 da Engr. Usman Ahmad Zun-Noorayne ya tattara daga wajen al’umma ya turo masa domin haɗawa da babban asusun tallafin.

Domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, Abba Hikima ya bayyana cewa ya miƙa wa Malam Haruna Bashir kwafin bayanan bankinsa (Statement of Account) na tsawon kwanakin da aka yi tattara kuɗin.
Haka kuma, ya sanar da cewa sun ziyarci bankin Malam Haruna inda aka rufe asusun (Block) na ɗan lokaci don tsaron lafiyar kuɗaɗen har sai komai ya lafa.

Sanarwar ta bayyana cewa an kammala tura kuɗaɗen ne a ranar Juma’a domin kauce wa jinkirin da karshen mako (Asabar da Lahadi) kan iya haifarwa a harkokin banki.

A ƙarshe, ya nuna godiyarsa ga dukkan al’ummar da suka ba da gudunmawa, tare da yin addu’ar Allah ya sanya albarka ga dukiyar, ya kuma sakawa kowa da alkhairi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *