Bayan Shafe Shekaru 74 Kamfanin Giya Na  Ya Sanar Da Ficewa Daga Najeriya

Screenshot 20240612 173458 Facebook

Kamfanin Guinness mai yin kayan sha ciki har da giya ya sanar da shirinsa na ficewa daga Najeriya saboda matsanancin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.

Kamfanin wanda ya kwashe fiye da shekara 74 yana aiki a Najeriya ya ce zai fice sannan kuma zai sayar da dukkannin hannin jari mallakarsa ga rukunin kamfanoni na Tolaram Group na ƙasar Singapore.

Alfijir labarai ta ta rawaito cewa kamfanin na Guinness dai ya yi asarar naira biliyan 61.9 a watan Yulin 2023 da Maris na 2024 bayan hawan Tinubu inda ya rage wa naira daraja.

Guinness Nigeria Plc, kamfani ne wanda yake cikin jerin sunayen kamfanoni da ke hada-hadar hannayen jari a Najeriya kuma an yi masa rijista a kasar a matsayin kamfanin da ke shigar da giya samfirin Stout daga Dublin.

People’s Gazette

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *