Bayan Ta Shirya Ayi Garkuwa Da Ita Don Karbar Kudin Fansa Yan Sanda Sun Kamata

FB IMG 1708502705355

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa-Ibom ta bayyana cewa ta kama batagari da a ciki akwai wata mata da ta hada baki da wasu maza hudu suyi a yi garkuwa da ita.

Alfijir labarai ta rawaito kwamishinan ‘yan sanda Waheed Ayilara wanda ya sanar da haka ya ce batagarin da suka kama sun kai mutum 52 sannan sun kama su bisa laifin fashi da makami wasu kuma ayyukan kungiyar asiri da damfara tare da safarar Kananan yara.

Kwamishinan ya ce matar da suka kama ‘yar asalin kauyen Nung Oku ne dake karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar.

Ya ce dakarun sun kama ta bisa laifin hada baki da saurayin ta domin yin garkuwa da ita inda har ta bukaci kudin fansa naira miliyan hudu.

Rahotanni sun bayyana cewa yan sanda sun samu labarin garkuwar ne bayan wani Enobong Sampson ya sanar da jami’an tsaron cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da ‘yar uwarsa kuma sun bukaci naira miliyan hudu kudin fansa.

“Nan da nan jami’an mu suka fara gudanar da bincike tare da tattaro bayanan sirri domin kamo mutanen.

“A ranar Talata dakarun suka kama matar tare da saurayinta a maboyar su dake Mbierebe Obio dake karamar hukumar Ibesikpo Asutan.

“Bayan sun shiga hannun jami’an tsaro matar ta tabbatar cewa ta hada baki da saurayin ta da wasu maza uku domin a yi garkuwa da ita.

“Matar ta ce ta yi haka ne domin ta samu kudi daga hannun goggonta dake zama a kasar waje.

Premium Times

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *