Bello Turji ya ƙuduri niyyar ajiye makamansa, sannan ya saki mutane 32 – In Ji Mal Asadus-Sunnah

FB IMG 1754400950741

Kasurgumin jagoran ƴan ta’adda a jihar Zamfara, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su tare da amincewa da ya dena kaiwa manoma hari, bayan ganawa da malaman addinin Musulunci a dajin Fakai, karamar hukumar Shinkafi.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Malamin addini Musulunci, Musa Yusuf, wanda ya fi shahara da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan a wani taron addini a Kaduna, inda ya ce al’ummar Shinkafi ne suka bukaci a shiga tsakani domin su samu damar komawa gonakinsu.

A cewar Yusuf, ganawar ta gudana sau uku a watan Yuli, kuma Turji da wasu fitattun mayaka kamar Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya, ciki har da ajiye makamai da barin manoma su koma gonaki ba tare da fargaba ba.

Yusuf ya ce wadanda aka sako sun hada da mata da yara, kuma sun shafe kusan watanni hudu a hannun Turji.

Wasu daga cikinsu sun haifi yara a daji, yayin da daya daga cikinsu ta kamu da cizon maciji.

Ya ce tun bayan yarjejeniyar, zaman lafiya ya fara dawowa a yankin Shinkafi, inda manoma ke ci gaba da aikin gona cikin kwanciyar hankali.

Malamin ya gargadi wasu malamai da ke sukar Turji a kafafen sada zumunta da su daina, yana mai cewa hakan na iya tayar da zaune tsaye.

Ya yabawa Shugaba Bola Tinubu,  Nuhu Ribadu, Gwamna Dauda Lawal da Sanata Shehu Buba saboda goyon bayan hanyar zaman lafiya wajen magance matsalar tsaro a Zamfara.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *