Biyan Kuɗi Yayin Shiga Itikafi A Masallatai Bidi’a Ce — In Ji Sheikh Maqari

FB IMG 1712230664574

Babban Limanin Masallacin Juma’a na Kasa, Farfesa Ibrahim Maqari ya yi tir da tsarin da wani Masallaci a Legas ya fito da shi na biyan kuɗi kafin mutum ya yi ibadar Itikafi a cikinsa.

Alfijir labarai ta rawaito limamin ya bayyana bacin ransa na wannan sabon abu da Masallacin ya fito da shi ne tare da yin sharhi mai tsawo kan haka a yayin tafsirinsa da ya ke yi a Babban Masallacin Juma’a na Kasa da ke Abuja.

Shehun Malamin ya kwantanta wannan mataki da masallacin na Legas ya fito da shi a matsayin wata sabuwar fitina a addini wacce ta fi kowacce bida’a muni a wannan zamani.

Wanda a cewarsa hakan zai iya haifar da fushin Allah kan wannan al’umma saboda kasuwantar da dakinSa ne wanda wasu addinai ke yi.

“Masallaci ɗakin Allah ne kuma da zarar mutum ya shiga, duk wani girma da ɗaukaka da muƙam8 da matsayi ya kare bakin kofa inda ya ajiye takalminsa.

“Duk wanda ke cikinsa daidai yake da kowa ba tare da banbancin mai shi da maras shi ba na dukiya ko matsayi.

“A inda zai iya zama a ko’ina kuma kusa da kowa. Amma sa kuɗi zai buɗe kofar nuna banbanci da matsayi wanda hakan ba musulunci bane,” in ji shi.

A yayin da yake amsa tambayoyi a ƙarshen tafsirin a inda wani ya bayar da hujjar Masallacin na karɓar kudi don kula da shi ne da kuma sayen Man dizel.

Sai Malam ya amsa da cewa hakan bai halarta ba.

“Sai dai in wasu ɗakuna aka ware a cikin masallacin wanda mutum zai kama ya zauna don yin Ibada wanda hakan ya halarta ko kuma kuɗin da ake biya na amfani da banɗakuna ne da za a shiga don biyan buƙata wanda da su za a kula da tsafta da gyaransa da kuma ma’aikata.

“Amma in don a shiga cikin Masallacin a yi Ibada ne kamar Itikafi ne sai an biya saboda a taƙaita yawan mutane, wannan bai halarta ba.

“Wanda kuma dole ne musulmai su haɗu su yaƙi wannan bida’a wacce ta fi duk wata bida’a da wasunsu ke ta suka muni saboda abin da hakan zai haifar a nan gaba,” in ji shi.

Jaridar Aminiya ce ta ba da rahotan Masallacin Juma’a na unguwar masu hannu da shuni na Lekki da ke Jihar Legas ya saka Naira 130,000 ga duk mai son yin Itikafi a cikinsa wanda hakan ya haifar da cece-ku-ce.

Kodayake, wannan ba sabon abu ba ne a jihar a cewar wani mazaunin garin kasancewar masallatai daban-daban na karɓar kuɗi kama daga Naira 10,000 zuwa 30,000.

Sai dai rahoton da aka samu dangane da kuɗin da Masallacin Lekki ya karɓa a wannan shekara ya zarce na kowa a jihar, lamarin da ya ja hankalny jama’a a ciki da wajen jihar.

Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *