Da Ɗumi Ɗuminsa! Gwamna Ya Dakatar Da Kwamishinansa Bisa Rashin Da a

Gwamnan jihar Ekiti Biodun Oyebanji ya dakatar da sabon kwamishinan masarautu da harkokin cikin gida Mista Olaiya Atibioke na tsawon makonni biyu.

Alfijir Labarai ta rawaito Atibioke na daya daga cikin karin kwamishinonin guda 19 da gwamna Oyebanji ya kaddamar a ranar Talatar da ta gabata, 8 ga watan Agusta.

Dakatarwar ta biyo bayan ficewar Mista Atibioke ba tare da izini ba daga wurin taron kwanaki uku na mambobin majalisar zartarwa ta jiha da sakatarorin dindindin da aka gudanar a dakin taro na Bishop Adetiloye Hall, Trade Fair Complex, Ado-Ekiti ranar Asabar.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman ga yan jarida Mista Yinka Oyebode, kwamishinan ya bar wurin taron ne ba tare da izini ba.

Ba a same shi ba a lokacin da aka kira kwamishinonin da su sanya hannu a kan takardar gudanar da ayyuka.

Gwamna Oyebanji ya zauna a dukkan zaman zaman na kwana uku wanda aka fara a ranar Alhamis.

Ya kasance, a yayin gabatar da jawabinsa, ya sake nanata yadda gwamnati ba ta jure wa rashin da’a da rashin aikin yi ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *