DA Ɗumi Ɗuminsa! Hukumar EFCC ta kama Willie Obiano Tsohon Gwamnan Anambra

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranar Alhamis ta kama tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos.

Obiano, wanda ke cikin jerin sunayen Hukumar, an kama shi da misalin karfe 8:30 na dare.

Rahotanni sun bayyana cewa yana kan hanyarsa ta barin kasar zuwa birnin Houston na jihar Texas ta Amurka.

Alfijr

Sauran bayanai na yafe, kamar yadda Channel Tv suka wallafa