Daga Aminu Bala Madobi
Shugaba Tinubu ya bukaci Mahmood da ya dakatar da dukkan aikinsa ya kuma tafi hutun dole na ƙarshe na barin hukumar.
Alfijir labarai ta rawaito wasu majiyoyi daga cikin gwamnati sun bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan abin da suka kira “cin amana a ƙarshe” da Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wa gwamnatin APC da ta naɗa shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Farfesa Mahmood Yakubu da ya tafi hutun dole tun kafin karewar wa’adinsa.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ziyarci Shugaba Tinubu jim kaɗan bayan dawowar shugaban ƙasa daga hutun aiki na kwana 12, inda ya koka da cewa Mahmood yana ƙoƙarin ƙara rijistar sabbin jam’iyyu a ƙarshen wa’adinsa, abin dake kokarin rikita shirin sake tazarcen Shugaba Tinubu.
Gwamnan ya kuma zargi shugaban INEC da goyon bayan wani ɗan takara a zaɓen gwamna na Imo.
Bayan wannan bayanai, rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya bukaci Mahmood da ya dakatar da dukkan aikinsa ya kuma tafi hutun dole na ƙarshe na barin hukumar.
Wannan mataki ya jefa hukumar INEC cikin tangal tangal da rudani, inda aka soke taron kwata-kwata na ƙarshe da shugabannin jam’iyyu da kuma wani taro da ake shirin yi da ƙungiyoyin farar hula.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai aike da sunan sabon Shugaban Hukumar Zabe INEC zuwa majalisar dokoki nan da kwanaki masu zuwa.
Mahmood Yakubu ya hau wannan kujerar ne a ranar 21 ga Oktoba, 2015 bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi, ya maye gurbin Amina Zakari wacce ke rikon kwarya a lokacin.
Binciken Karkashin Kasa Da Jaridar Alfijir Ta Gudanar ya Muna cewa tsohon Gwamnan Delta, James Ibori na kan gaba, da ka iya lallasar Shugaba Tinubu ya amince da wani Dan Lelen sa daga yankin Oghara ta jihar Deltan, Moses Ogbeh, a matsayin sabon Shugaban Hukumar zabe, wanda hakan zai ba su damar shirya kowacce irin manaƙisa da ƙulunboton saita alƙaluman cin zabe tuwona maina
Abin jira, lokaci. *ABM*
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t