Dole Mu kare Mutuncin Sarkin Musulmi, Shettima Ya Gayawa Gwamnatin Sokoto

FB IMG 1719250116527

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bukaci gwamnatin jihar Sokoto da ta bawa mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III kariya, da mutunci. Ya jaddada hakan ne a taron zaman lafiya da tsaro na yankin Arewa maso Yamma, wanda aka watsawa kai tsaye a gidan talabijin na Trust daga jihar Katsina.

“Ubanmu, wanda ya kasance mai dawwama a cikin dukkan al’amuran ci gaban kasar nan, Mai Martaba Sarkin Musulmi, dole ne a kare mutuncin sa da kuma yaba masa. Ga Mataimakin Gwamnan Sakkwato, ina da sako mai sauki: Eh, Sarkin Musulmi Sarkin Musulmi ne, amma ya fi haka; Yana wakiltar ra’ayi. Shi cibiya ce da dukkan mu a kasar nan ya kamata mu kiyaye da kishi, kariya, ingantawa, kiyayewa, da aiwatar da ayyukan al’ummarmu,” in ji Shettima.

Alfijir labarai ta ruwaito Shettima ya bayyana haka ne bayan babban daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Isiaq Akintola, ya yi zargin cewa Gwamnatin Sakkwato na shirin tsige Sarkin Musulmi. A baya Gwamna Ahmed Aliyu ya kori sarakunan gargajiya 15 bisa wasu laifuka.

Sai dai har yanzu Gwamnatin jihar Sokoto ba ta mayar da martani kan zargin MURIC ba. A baya ta bayyana shirin yin kwaskwarima ga sashe na 76 na dokar kananan hukumomi da masarautu domin yin daidai da al’amuran da ke faruwa a jihar. A tsarin dokar da ake da shi yanzu, ikon nada hakimai da kauyuka yana hannun Majalisar Sarkin Musulmi ne, wadda ta ba da shawarwari ga gwamnatin jihar, inda daga karshe gwamnan ya nada.

Nasir Binji, babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar, ya fayyace cewa gyaran da aka gabatar na da nufin daidaita tsarin shari’a da tsarin al’ada a Sakkwato.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar, Binji ya bayyana cewa, a karkashin shirin gyaran da aka yi, Majalisar Sarkin Musulmi za ta ci gaba da rike madafun iko na ba da shawara ga ‘yan takara, yayin da kuma ikon nada shi zai kasance ga gwamna.

KBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *