Dr Faruq Umar Magatakardan Hukumar Lura Da Aikin Jinya Da Unguwanzoma ta Nijeriya Ya Magantu Kan Farfesa Adamu Gwarzo

IMG 20231219 WA0191

Daga Ali Kakaki

Magatakardan Hukumar Lura Da Aikin jinya da Unguwanzoma na Nigeriya Dr Faruq ya yi wannan furucin ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan da kammala bikin rantsar da daliban da suka yi karatun jinya daga kasashe daban-daban na duniya. Karo na Goma sha Daya, (11) wanda aka Gudanar a Dakin taro na jamiar maryam Abacha Amerikan University dake birnin kano,

Sannan har wala yau ya kuma bayyana Farfesa Gwarzo da cewa mutum ne mai karamci, domin ya karrama su kuma sun gani a aikace; “ya karrama mu ya mutunta mu, duk abin da ake yi ma bako a faranta masa ya yi mana. Kuma tsare-tsaren da aka yi, babu bambanci da cewa taron da aka yi a Abuja ne aka yi shi”.

Ya ce za su rika kai taron rantsar da dalibai sassa daban-daban na kasar, kuma yadda suka ga taron na bana a Jami’ar Maryam Abacha American University, sun yaba matuka.

Ya kuma yi kira ga daliban da su ji tsoron Allah; “aikin nan da kuka yi karatu domin shi ku gudanar da shi ta yadda su al’umma za su bambance ma’aikacin jinya da wanda ba na jinya ba. Amfanin ilimi ka kawo canji. Al’umma na da korafi ga ma’aikatan jinya, ilimi shi zai kawo canji. Ku yi amfani da wannan basirar ilimin da kuka samu domin kawo canji ga al’umma kan matsayin yadda suke yi wa ma’aikatan jinya kallo”, ya jaddada.

Dr. Faruq ya ce akwai bukatar daliban su sauya tunanin al’umma domin su fahimci cewa aikin jinya aiki ne na kawarai da kuma taimakon al’umma da kawo ci gaba ga mara lafiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *