Dubun Wani Barawo Mai Canjawa Mutane ATM A Wajen Cirar Kudi Ta Cika

Alfijr ta rawaito rundunar yan sanda ta jihar kano ta samu nasarar Kama wani matashi mai suna Gaddafi jibrin mai shekaru 33 dake unguwar tudun murtala a kano.

Gaddafi ya shiga hannu ne bayan da akayi wa yan sandan Korafi akansa ya canjawa wani mutum ATM ya bashi na Bogi lokacin da ya nemi ataimaka masa wajen cire kudi.

ALFIJR

Yan sandan sun sami nasarar kama Gaddafi da ATM 22 da kuma mota kirar peaugeut wadda sukeyin amfani da ita wajen zagayawa wuraren da ake amfani da ATM domin cutar al’umma.

Da yake holensa gaban manema labarai DSP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, Gaddafi ya amsa laifinsa kuma ya tabbatar da bashi kadai yake wannan aikin ba, Kiyawa ya tabbatar da baza jam’i an tsaro ko ina a jihar nan don kamo ragowar bata garin.

ALFIJR

Kiyawa ya shawarci mutane da su daina neman taimakon cire kudi ga Wanda basu sani ba, su zo da yan uwansu ko kuma meni ma aikacin bankin, domin gujewa irin wadannan bata garin

Slide Up
x