Dubun Wani Zangina Ta Cika Yayin Da Aka Kama shi Ya yiwa Yarinya Yar 18, Fyade Nassarawa

  ‘Yan sanda sun kama wani mutum da ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 18 fyade a Nasarawa

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Matashin mai suna Mohammed Zangina ya shiga hannu ne a garin Kefii da ke jihar Nasarawa bisa zarginsa da yin zagon kasa da lalat wata matashiya yan shekara 18 da haihuwa. 

The Punch ta rawaito, wani dan jarida, Gimba Kakanda – @gimbakakanda, wanda ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya bayyana cewa, Zangina, mai aure ne da yaya biyu, ya sha yi wa yarinyar mai shekaru 18, barazana da hotuna tsiraici. 

An ce mutumin da aka kama ya bukaci yin lalata da ita, kafin a kama shi a kai shi hedikwatar ‘yan sanda da ke Keffi. 

An bayyana cewa mutumin yana da hotunan wasu mata a wayarsa Kala kala irin wadanda yake sakawa a tarkinsa.

 Best seller channel

 Duk da cewa an yada hotuna da bidiyo na kama mutumin a ofishin ‘yan sanda, amma kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Nasarawa bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto. 

Sai dai Kakanda ya bayyana cewa an kama mutumin ne tare da taimakon jami’an ‘yan sanda, wadanda ya ce kwararru ne a aikinsu.

 Kakanda ya wallafa cewa, “Bayan da ya yi wa wata yarinya ‘yar kasa da shekara 18 fyade a baya, sannan ta aika masa kudi, Mohammed Zangina ya yi barazanar sakin tsiraicin ta a hannun sa matukar ba za ta iya zuwa Keffi domin yin lalata da shi ba. 

  Lokacin da aka ce yarinyar ta kai masa ziyara zuwa Keffi daga garinsu mai nisa kamar yadda ya bukata, ya sa ta ci gaba da daukar hotunan abubuwan da ke kewaye da ita a tsawon tafiyarta. 

 A lokacin da suke hira, sai ya ci gaba da umurtar yarinyar data dinga motsa sassan jikinta, yayin da shi kuma gogan yake kallo tare da daukar hotonta. 

Bisa rahoton sirri da nuna kwarewa aikin Yan Sanda aka kama shi aka kaishi  ofishin ‘yan sanda. 

Best Seller Channel 

A binciken wayarsa da  aka yi an gano yana da tsiraicin mata da yawa  ajiye a wayarsa, wanda yanzu haka yana hannun ‘yan sanda. 

Yayin binciken an tabbatar da ya sha kwaya kala-kala a shirye-shiryen ziyarar yarinyar. 

Mai laifin ya ce yana da mata da ’ya’ya biyu.

Slide Up
x