Dubun Wasu Ma’aikatan Hukumar RMAFC Ya Cika Bisa Zargi Yin Kutse A Tsarin IPPIS


Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban hukumar raba daidai da tarawa gwamnatin tarayya haraji (RMAFC) Dakta Muhd Bello Shehu, ya tabbatar da bankado wasu ma’aikatan hukumar bisa zarginsu da yin kutse a cikin tsarin biyan ma’aikata albashi na IPPIS.

Ma’aikatan sun yi kutsen ne don kara wa kansu yawan albashin da gwamnati ke biyansu.

Dakta Bello, wanda ya bayyana wa manema labarai hakan, ya ce, an dakatar da wadanda ake zargin har sai an kammala bincike kan zargin, inda ya ce, idan an same su da aikata wannan badakalar da ake zarginsu, za a mika su ga mahukuntan da suka dace, don hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

An fara zargin badakalar ne yayin da wani ma’aikaci a mataki na 7 a tsarin biyan albashin gwamnati, wanda ya kamata ya amsa naira N60,000 amma aka biyashi naira N400,000 dai-dai da albashin Darakta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *