Hukumar EFCC ta kama tsohon dan majalisar wakilai, Gudaji Kazaure bisa zargin karbar Naira miliyan 70 daga hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.
Majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa din sun kama Kazaure a jiya Laraba jim kadan bayan wata babbar kotu a Kano ta janye umarnin hana kama tsohon dan majalisar.
A cewar wata majiya a hukumar ta EFCC, Kazaure ya karbi Naira miliyan 20 a kashi biyu ta hannun jakadan Emefiele mai suna Eric domin sayen “ragon sallah”.
Majiyar ta ci gaba da cewa Kazaure daga baya ya karbi kudi Naira miliyan 50 a matsayin “gudunmawa” daga Emefiele, biyo bayan wata gobara da ta tashi a gidan tsohon dan majalisar.
Majiyar ta ce a halin yanzu Kazaure na tsare a ofishin hukumar da ke Kano kuma ana iya kawo shi Abuja domin fuskantar tuhuma.
A tuna cewa watan Disambar 2022 ne dai Kazaure ya zargi gwamnan CBN na lokacin da cin-hanci, inda ya yi zargin cewa Naira tiriliyan 89.1 na ‘Stamp Duty’ sun yi ɓatan-dabo a karkashin Emefiele ɗin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD