EFCC Ta Damke Wani Ɗan Najeriya Da FBI Ta Amurka Ke Nema Ruwa A jallo

Alfijr ta rawaito Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta cafke wani da ake zargi da damfara, Emmanuel Dike Chidiebere. Chidiebere ya kasance cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo na Hukumar Bincike ta Tarayya (FBI).

Ana zarginsa da hada baki da zamba da kuma karkatar da kudade.

Bayan samun bayanan sirri, EFCC ta bi sawun sa zuwa karamar hukumar Orlu ta jihar Imo inda aka kama shi.

Ana zargin Chidiebere da damfarar wasu ‘yan kasar Amurka da Cote D’Ivoire da kuma Poland.

Ya yi layar zana bayan ya tsere musu da makudan kudade abinsa.

Uku daga cikin abokansa har yanzu ba a kama su ba, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa a makon da ya gabata, an kama wani wanda ake zargi da hukumar FBI ke nema ruwa a jallo, Kelechi Vitalis Anozie.

Ɗan Damfarar Shi ne ya kafa cocin Praying City Church a Owerri, babban birnin Imo.

Makwanni biyun da suka gabata, Osondu Victor Igwilo, wanda shi ma yana cikin jerin sunayen FBI tun 2018, an kama shi a wani studio a Lagos.

An kama Igwilo ne tare da Okafor Nnamdi Chris, Nwodu Uchenna Emmanuel da John Anazo Achukwu a yankin Sangotedo.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *