Farfesa Adamu Gwarzo Ya Bayyana Rasuwar Haj Atika Wammako Babban Rashi Ne Ga Al’umma

Alfijr ta rawaito Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University of Niger (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajantawa Sanata Aliyu Wamakko, Magatakarda Wamakko bisa rasuwar matarsa, Hajiya. Atika.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano.

Farfesa Gwarzo ya bayyana rasuwar Hajiya Atika a matsayin babban rashi ba ga danginta kadai ba har ma da daukacin al’ummar jihar Sakkwato.

“A cikin zucciyar zuciya muka samu labarin rasuwar uwargidan ka, Hajiya Atika, a madadin ‘yan uwana da Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), ina mika sakon ta’aziyyarmu a gareku, bisa rasuwar matarka.

“Ina kuma so in yi amfani da wannan dama wajen jajantawa daukacin al’ummar Jihar Sakkwato bisa wannan babban rashi da aka yi, Allah Madaukakin Sarki Ya ba ku ikon jure wannan rashi mara misaltuwa.” Inji Farfesa Gwarzo

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *