Fastar yakin neman zaben shugabancin kasa ta Ganduje/Uzodima ta karade shafukan sadarwa

Screenshot 20240818 184054 Facebook

Fastar tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ta neman tikitin takarar shugaban kasa na hadin gwiwa a 2027, sun taso a shafukan sada zumunta.

Fastocin sun nuna cewa Ganduje wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa a yanzu, zai tsaya takarar shugaban kasa, yayin da Uzodinma wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC, zai kasance mataimakinsa.

Fastocin da ke dauke da taken, ‘Ga ‘yan Najeriya, wadata da ci gaban bil’adama’ sun kuma nuna cewa ‘yan siyasar biyu za su fafata a zaben 2027 a karkashin jam’iyyar APC.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙura ta taso kan yunkurin tsige Ganduje daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa domin neman mukamin jakadanci, ikirarin da kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa (NWC) ya bankado a matsayin karya.

Sai dai kuma da ya ke mayar da martani, Ganduje ya bayyana fastocin a matsayin aikin yan adawa.

Edwin Olofu, Babban Sakataren Yada Labarai na Ganduje, a wata tattaunawa ta wayar tarho da Daily Trust ya ce, “Abin dariya ne kuma yarinta ne, kuma aiki ne kawai na yan adawa.

“Irin su ne suka dage sai an cire shi (Ganduje) a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

“Wannan shiri ne da gangan don haifar da rashin jituwa tsakaninsa da dan uwansa kuma jagoransa, Bola Ahmed Tinubu. Amma su na bata lokacin su ne domin daina yin barna domin Shugaba Tinubu ya fi karfin shiga irin wadannan shirmen .”

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *