Gwamna Yusuf ya naɗa mai jawa Sheikh Karubullah Nasiru Kabara baki a gidan Sarki ,da Sheikh Ali Dan Abba da Sheikh Dan Almajiri mukamai
Gwamnan jihar Kanoi Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Shugabannin hukumar shari’a da zakka a jihar Kano.
A yayin kaddamar da shugabanin hukumar ta shari’a, gwamna Yusuf ya nada sheikh Abbas Abubakar Daneji a matsayin Shugaban hukumar ta shari’a.
Gwamna Yusuf ya nada mutane 16 da zasu jagoranci hukumar ta shari’a ciki harda shugabanta Sheikh Daneji.
Sauran Shugabannin hukumar shari’ar sun hada da Sheikh gwani Hadi Gwani Dahiru a matsayin kwamishina na daya da Sheikh Ali Dan Abba a matsayin kwamishina na biyu.
Sai Kuma Shiek Abubakar Mai Ashafa a matsayin Mamba,da Malam Naziru Saminu Dorayi shima Mamba da sauransu.
Yayinda kuma Dr Muhammad Sani Hashim zai kasance Sakataren hukumar ta Shari’a.
A bangaren hukumar zakka da Hubusi,Kuma gwamna Yusuf ya nada Sheikh Barista Habibu Dan almajiri a matsayin Shugaban hukumar ta zakka.
Sauran mutanan sun hada da Sheikh Nafiu Umar Harazimi a matsayin Kwamishina na daya sai kuma Dr Ali Kurash a matsayin Kwamishina na biyu da sauransu.
A yayinda yake jawabi jim kadan da mikawa mutanan takardar kama aiki ,yace ya zabo sune a bisa cancanta da gogewarsu.
Ya horesu da su bada hadin kai wajen ciyar da Kano gaba.
Yace musamman hukumar zakka a kano yana mai cewa duk da arzikin da al’umar kano kedashi Amma abin haushi har yanzu mutane suna bara.
Gwamna Yusuf yace duk Najeriya babu wata jiha a Najeriya da take da attajirai sama da Kano,a dan haka ya bukaci hukumar ta zakka ta tashi tsaye domin ganin ta sauke nauyin da aka dora mata.
Gwamnan yace akwai tabbacin,nan da wani lokaci ,Mutanan kano musamman manyan masu kuɗi zasu rika tururuwa wajen ganin sun mika zakka domin fitar da jama’ar kano daga cikin talaucin da ake ciki.
Sannan itama hukumar shari’a ta Kano, gwamna Yusuf ya nemi hukumar da tayi aikinta abisa gaskiya da rikon amana da Kuma adalci.
Daga nan gwamna Yusuf ya godewa Hukumar Hisba ta jihar Kano abisa kokarinta na ganin an kyautata rayuwar jama’a musamman ragaitar kananan yara a birnin Kano.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ