Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sake fasalin majalisar zartarwarsa tare da ƙirƙirar sabuwar Ma’aikatar Harkokin Kiwo domin inganta gudanar da ayyukan gwamnati a jihar.
Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Ibrahim Kaula-Mohammed, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Katsina.
A cewar sanarwar, Gwamna Radda ya amince da sauyin mukaman kwamishinoni da kuma nada wasu sabbin kwamishinoni domin ƙara inganta gudanar da ayyukan gwamnati a muhimman fannoni.
A cikin sabon tsarin, an tura Adnan Nahabu daga Ma’aikatar Harkokin Musamman zuwa Ma’aikatar Ilimi mai zurfi, Fasaha da Sana’o’i, a matsayin kwamishina. Haka kuma, Farfesa Ahmad Muhammad-Bakori, wanda ya kasance a Ma’aikatar Noma da Ci gaban Kiwo, yanzu shi ne zai jagoranci sabuwar Ma’aikatar Harkokin Kiwo.
Alhaji Aliyu Lawal-Zakari, wanda ya kasance a Ma’aikatar Matasa da Wasanni, an tura shi zuwa Ma’aikatar Noma, yayin da Hajiya Zainab Musa-Musawa daga Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta koma Ma’aikatar Harkokin Musamman.
Haka kuma, Alhaji Yusuf Suleiman-Jibia, ya zama sabon Kwamishina na Ilimin Firamare da Sakandare, yayin da Alhaji Surajo Yazid-Abukur aka nada shi Kwamishina na Matasa da Wasanni.
Sannan Aisha Aminu, tsohuwar Darakta-Janar na Hukumar Ci gaban Sana’o’in Jihar Katsina (KASEDA), ita ce sabuwar Kwamishiniyar Harkokin Mata.
A gefe guda, Hajiya Hadiza Abubakar-Yar’adua daga Ma’aikatar Harkokin Mata, an tura ta ta zama Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Abinci mai Gina Jiki da Walwalar Jama’a, yayin da Isa Muhammad-Musa daga Ma’aikatar Ilimi mai zurfi, Fasaha da Sana’o’i, aka nada shi Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Al’adu.
Gwamna Radda ya yi kira ga dukkan sabbin kwamishinonin da su kasance masu jajircewa da gaskiya wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa ta “Building Your Future Agenda”, tare da mai da hankali kan hidima ga jama’ar jihar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t