Gwamnatin Jihar Borno ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a fadin jihar.

FB IMG 1722516671454

An dauki matakin ne bayan wani harin bam da aka kai a Konduga da kuma zanga-zangar da ta rikide ta koma tashin hankali a sassan birnin.

Alfijir labarai ta ruwaito a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Kenneth Daso ya fitar, ya ce gwamna Babagana Zulum ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro na jihar.

“A bisa umarnin da tsarin mulki ya ba mu na maido da doka da oda, mai girma Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umar Zulum bayan tuntubar shugabannin tsaro a jihar ya ga dacewar  sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 nan take”. Inji ASP Daso.

Sanarwar ta ce, harin bam di  ya yi sanadiyar mutuwar mutane 16 yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka kuma a halin yanzu suna samun kulawa a cibiyoyin lafiya.

“Kuna sane da lamarin da ya faru a garin Kamari wato tashin bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane (16) yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka inda aka garzaya da su a asibitoci daban-daban na gwamnatin jihar.”

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda a duk tsawon lokacin dokar ta hana fita.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *