Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Tsarin Sufuri na Zamani Don Inganta Tsaro da Saukaka Harkokin Zirga-zirga

IMG 095250 291225 1766998393478

Gwamnatin Jihar Kano ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin Kirkire-kirkiren fasahar sadarwa na AS and AJ Multi Services  domin kaddamar da tsarin sufuri na zamani da ke amfani da fasahar sadarwa don dakile ayyukan batagari da inganta tsaro a fadin jihar.

An gudanar da bikin rattaba hannun ne a  ofishin Ma’aikatar Harkokin Sufuri, inda Kwamishinan Sufuri, Barista Haruna Isah Dederi, ya bayyana cewa wannan mataki wata babbar nasara ce ga jihar wajen sauya fasalin sufuri da tabbatar da tsaro.

Dukkan mai mota dole ne ya samu na’urar bin diddigi (tracker) ya sanya ta a motarsa. Wannan zai ba da damar bibiyar motar da kuma mai ita, wanda hakan zai kara tsaro a fadin Kano,” in ji Dederi.

Kwamishinan ya bayyana cewa duk masu ababen hawa a jihar za a bukace su da su sanya na’urorin bin diddigi domin a rika bibiyar motsin su a ainihin lokaci.

Ya ce hakan zai taimaka wajen dakile laifuka da ta’addanci ta hanyar samar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa wannan shiri wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na hada fasaha da harkokin sufuri domin inganta rayuwar al’umma.

Karanta LabariGwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Kar-ta-Kwana Don Tunkarar Matsalolin Tsaro a Kano

“Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da wannan kwangila a ranar 19 ga Disamba, 2025, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro,” in ji shi.

Wannan ci gaba ya sanya Kano a sahun gaba wajen aiwatar da sabbin hanyoyin sufuri masu amfani da fasaha a Arewacin Najeriya, tare da yiwuwar zama abin koyi ga sauran jihohi.

A nasa jawabin, Shugaban Kamfani na AS and AJ Multi Services, Alhaji Abdulkarim Abdullahi, ya bayyana cewa tsarin zai kunshi wata manhaja mai suna Sufuri Transport da za ta saukaka harkokin Keke Napep da tabbatar da tsaro.

Karanta Labari: Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano

“Za a rika bai wa jami’an KAROTA takardun shaida (stickers) domin tantance motoci da direbobi. Kowanne direba zai kasance da na’urar bin diddigin da ke da alaka da Keke Napep dinsa da kuma mai motar,” in ji Abdullahi.

Muhimman Abubuwan Da tsarin zai kunsa sun hadar da: Rajistar Direbobi da Motoci: Kowanne direban Keke Napep za a yi masa rajista ta hanyar fasaha tare da danganta shi da motarsa da mai ita.

Takardun Tantancewa: Jami’an KAROTA za su rika amfani da takardun shaida na musamman domin tabbatar da sahihancin direbobi da motocin haya.

Manhajar Fasinja: Ta hanyar Sufuri Transport, fasinjoji za su iya gano Keke Napep mafi kusa, yin ajiyar tafiya a lokaci guda, da biyan kudi ta waya, kati ko kudi kai tsaye.

Abdullahi ya bayyana cewa na’urorin bin diddigi za su kasance a bude ga kowa da kowa, kuma suna da matukar muhimmanci wajen gina tsarin tsaro da gwamnatin Kano ke aiwatarwa.

“Wannan shiri ba wai na sufuri kadai ba ne, yana da nasaba da tsaro, gaskiya da kuma zamani. Daya ne daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin rage matsalolin tsaro da kuma inganta rayuwar yau da kullum ta al’ummar Kano,” in ji shi.

Ya jaddada cewa ana sa ran tsarin zai hana aikata laifuka ta hanyar bibiyar motsin motoci a ainihin lokacin, da kuma inganta dokokin zirga-zirga da aiwatar da su yadda ya kamata.

“A hadin gwiwar Ma’aikatar Sufuri, KAROTA da AS and AJ Multi Services, Kano na kan hanyar zama abin koyi a fannin sufuri na zamani a Najeriya,” ya jaddada.

Justice Watch

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *