Gwamnatin Kano Ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kansa A Jihar

IMG 20240420 WA0111

Hukumar dake kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe wani asibiti mai suna Sassauka Clinic and Diagnosis Centre, dake unguwar Rimin Kebe.

Alfijir Labarai ta rawaito babban daraktan hukumar ta PHIMA, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon saba wasu dokokin hukumar da asibitin ke yi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Ibrahim Abdullahi ya sanyawa hannu.

Farfesa Salisu ya bayyana cewa an sauyawa asibitin suna ba tare da sanar da hukumar ba, Inda yace da farko hukumar ta yiwa asibitin rajista ne da sunan Sassauka Clinic and Diagnosis, amma yanzu kuma asibitin ya koma yana amfani da wani sunan na daban inda ya koma Sassauka Hospital ba tare da neman sahallewar hukumar ba, wanda hakan ya sabawa doka.

Shugaban hukumar ya kara da cewa an kuma kara fadada asibitin daga mai gado shida ya koma mai Gado 40 ba tare da sun sanar da hukumar ba, wanda shi ma hakan ya sabawa dokar hukumar.

Ya kuma bayyana cewa, a dokar hukumar duk asibitin da yake da gado 40 dole ne ya samar da akalla likitoci guda 3, Amma yace su asibitin Sassauka har yanzu likita daya ne ke kula da shi kuma shi ma ba kullum yake zuwa ba.

Farfesa ya koka da cewa hatta ma’aikatan da ke tallafawa wajen tafiyar da asibitin sun yi ƙaranci kuma hakan yasabawa ka’idar aiki.

Shugaban ya ce saboda wadancan laifukan da aka lissafa ne yasa suka rufe asibitin kuma suka gayyaci mai asibitin zuwa hukumar a mako mai zuwa domin daukar matakan da suka dace akan shi.

Daga nan sai shugaban ya nanata kudirin hukumar PHIMA na ci gaba da tsaftace ayyukan asibitoci masu zaman kansu a jihar, inda ya bukace su da su ba hukumarsu hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ke samar da ingantacciyar hidimar kiwon lafiya ga jama’a.

Ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kyakkyawar kulawar da ya baiwa tsarin kiwon lafiya na jihar ta hanyar samar da kayan aiki da ake bukata domin farfado da fannin domin ya dace da tsarin aikin kula da lafiya a duniya.

Farfesa Salisu ya kuma yaba da irin goyon baya da jagoranci da Kwamishinan Lafiya Dokta Abubakar Labaran ya bai wa hukumar ta PHIMA da sauran hukumomin da ke karkashin ma’aikatar wajen gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma musu baki ba .

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *