Gwamnatin Jihar Kano tayi alkwarin kammala manyan ayyukan gine-gine guda biyu wato gadar sama ta Tal’udu da ta Dan’Agundi kafin ƙarshen wannan shekara.
Kwamishinan ma’aikatar bibiyar ayyukan gwamnatin jiha Hon.Nura Iro Ma’aji ya bayyana hakan, ya ce ana gudanar da aikin ne da tsari mai karfi domin tabbatar da cewa an gama da inganci kuma akan lokaci.
Da zarar an kammala aikin Gadojin za’a kaddamar da fara amfani da su a watan Janairu na 2026 domin inganta tattalin arzikin jama’ar Kano da ma makota.
Rahotanni sun nuna cewa aikin gadar Tal’udu, zuwa yanzu ya kai kimanin kashi 60 cikin 100, yayin da gadar Dan’Agundi ta kai kusan kashi 70 cikin 100 a halin yanzu.
A cewar kwamishinan, waɗannan manyan gadoji biyu waɗanda jimillar kuɗinsu ta kai Naira biliyan 27 za su taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano, tare da inganta tsarin zirga-zirgar jama’a.
Idan zaki iya tunawa an fara aikin gadar Dan’Agundi ne a watan Disamba na shekara ta 2023, yayin da aikin Tal’udu shi ma aka fara shi a daidai wannan lokaci.
Wannan aikin na daga cikin manyan shirye-shiryen gwamnatin Kano na inganta ababen more rayuwa da rage cunkoson hanyoyi a birnin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t