Gwamnatin Kano ta ware kusan miliyan 67, domin horas da ma’aikatan jihar masu matakin 13 zuwa 14, ASCON

IMG 105344 211025 1761040438124

Shugaban ma’aikatan jahar Kano Abdullahi Musa yaja hankalin ma’aikata kan zuwa aiki akan lokaci a fadin jihar, domin sauke alkawarin da kowa ya dauka da kansa.

Wannnan na zuwa ne yayin taron shirin horas wa da za’a yiwa ma’aikata masu mataki na 13, zuwa 14 wato ASCON a ranar 27th ga watan Oktoba 2025 a makarantar SAS dake Kano, mutum 485.

Musa ya godewa Allah kan yadda gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ya sahale a kashe kusan miliyan 67, domin a horas da ma’aikatan Kano domin samun gogewa ta musamman a jihar.

Hakazalika Abdullahi Musa ya nuna jin dadinsa na yadda aka dawo na wannan horaswar bayan dogon lokaci da aka daina bada wannan horo a jihar.

Ya kuma tabbatar da cewar za ayi wannan jarrabarwar ne cikin tsari da adalci, babu maganar wata sanayya ko kusanci a cikinta.

Shima a nasa bangaren famanan sakatare na hukumar ma’aikatan jihar Kano Alh Salahudden Habibu Isa yayin jawabin maraba, ya ja hankalin ma’aikata kan tsayawa da jajircewa kan ayyukan su tsakanin su da Allah kamar yadda suka yi alkawari yayin karbar takardar kama aiki.

Hakazalika ya gode gwamnan Kano kan yadda da amincewa akan dawo da wannan horaswar, saboda mahimmancin ta a wajen ma’aikata, bayan kiraye-kirayen da ake ta yi a faɗin jihar

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *