Gwamnatin Nijar ta dakatar da sarkin Sakorbe da ke jihar Dosso daga matsayin sa

IMG 112244 291225 1767003788390

Wannan mataki ya biyo bayan wadansu kalamai ne da sarkin ya yi a cikin wani faifan murya da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ne ,aka ji Sarkin na Sokorbé mai martaba MOUSSA MADOUGOU DAKAOU,na furta wasu kalamai da mahakuntan ƙasar suka ce, na baraza ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

A cikin kalaman na sa ,sarkin, ya yi zargin cewa ne ,an tafaka rashin adalci akan batun kokowar da  NOURA HASSAN na Tahoua, ya kayar da ISSAKA ISSAKA na Dosso.

Ƙoƙarin mahukunta na ganin waɗannan kalaman ba su tada ƙura a tsakanin yan ƙasar ba ne ya sa ,gwamnatin ƙasar ta fuskar ma’aikatar cikin gida ta ɗauki matakin dakatar da  sarkin daga muƙaminsa ,kafin gama ɗaukar matakan da suka kamata.

Dalilai da yawa ne ofishin ministan cikin gidan ya dogara da su wajen ɗaukar wannan matakin, musamman ma irin ta’asirin da ke da Sarki a cikin al’umma, kuma a ce ya yi irin wannan furucin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *