Hajj 2024: ICPC ta tabbatar da kama jami’an hukumar NAHCON

FB IMG 1723317663301

Hukumar Yaki da Ayyukan Cin hanci da Dangoginsu, ICPC, ta tabbatar da cewa ta na bincikar hukumar Aikin Alhazai ta Ƙasa, NAHCON kan tallafin Naira Biliyan 90 na aikin Hajjin 2024.

Alfijir labarai ta ruwaito Demola Bakare, mai magana da yawun hukumar ICPC ne ya shaidawa TheCable cewa hukumar ta kama jami’an NAHCON a ranar Laraba bayan sun ki amsa gayyata.

Bakare ya kuma musanta cewa sun rufe ofishin NAHCON din,  inda ya yi bayanin cewa su na aiki ne bisa doka.

Sai dai yaki bayyana sunayen jami’an da su ka kama amma ya ce suna taimakawa hukumar ICPC da gamsassun bayanai.

“Muna bincikar jami’an hukumar kula da aikin Hajji ta kasa saboda sun ki amsa gayyata. Mun kuma kai musu ziyara”,  inji shi.

“Bamu rufe ofishin hukumar ba kamar yadda wasu ‘yan jarida ke fada. ICPC na aiki ne bisa doka”.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ta NAHCON, Fatima Usara ta ce ba sabon abu ne yin tambayoyi ga jami’ansu bayan kammala aikin Hajji.

A watan Yuli dai, hukumar EFCC ta gayyaci shugaban hukumar EFCC kan zargin badakala a aikin Hajjin na 2024.

The Cable

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *