Hannatu Musa Musawa Tayi Martani Mayar Da Martani Kan Hukumar NYSC

Musawa, wadda a halin yanzu tana aikin bautar kasa na shekara daya, tana rike da mukamin minista wanda hakan ya karya dokar NYSC.

Alfijir Labarai ta rawaito Ministar kere-kere, al’adu da tattalin arziki, Hannatu Musawa, ta mayar da martani kan rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa ita ma’aikaciyar hidimar kasa ce a hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).

Musawa ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu a ranar Lahadi, inda ta jaddada cewa a halin yanzu ita mambar NYSC ce wadda ba ta saba wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ba.

Idan dai za a iya tunawa, daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, ta bayyana cewa Musawa, wadda a halin yanzu tana aikin bautar kasa na shekara daya, tana rike da mukamin minista wanda hakan ya karya dokar NYSC.

Da yake zantawa da wakilin Aminiya ta wayar tarho, Megwa ya tabbatar da cewa ministar ta shafe watanni takwas tana aiki a babban birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa ya sabawa dokar NYSC duk wani dan bautar kasa ya karbi duk wata nadin gwamnati har sai an kammala hidimar shekara daya.

Ya ce tun a shekarar 2001 Musawa ta fara hidimar bautar kasa, a jihar Ebonyi inda ta yi shirin wayar da kan ta amma daga baya ta koma jihar Kaduna domin ci gaba da shirin. Sai dai bata samu damar kammalawa ba a wanchan lokacin.

Haannatu da take mayar da martani a ranar Lahadin da ta gabata, sabuwar ministar da aka nada ta ce ba za ta iya kammala shirin ba saboda hakkin iyali da ta fuskanta a lokacin.inji Barrister Hannatu Musawa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *