Hannayen Jarin kamfanonin Faransa Sunyi Faduwar Bakar Tasa Bayan juyin Mulki A Gabon

Faransa ta ce tana sanya ido sosai a kan halin da ake ciki a Gabon.

Alfijir Labarai ta rawaito hannaye jarin kamfanonin Faransa uku sun fadi a kasuwar hada-hadar hannun-jari ta Paris ranar Laraba bayan sojoji sun sanar da kifar da gwamnati a Gabon, inda suke gudanar da harkokinsu.

Hannayen-jarin kamfanonin Maurel & Prom, Eramet, da reshen TotalEnergies na kasar Gabon sun fadi da kashi 15 zuwa 20, a cewar jaridar Les Echos da ake wallafawa a kowace rana a Faransa.

Tun da farko kamfanin hakar ma’adinai na Eramet ya sanar cewa ya dakatar da ayyukansa da kuma sufurin jiragen kasa a Gabon.

Wasu manyan sojojin Gabon sun bayyana a gian talabijin da sanyin safiyar Laraba inda suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo.

Sanarwar tasu na zuwa ne jim kadan bayan hukumar zaben kasar ta ayyana Shugaba Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben karo na uku indaya samu kashi 64.27 na kuri’un da aka kada.

TRT Africa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *