Hukumar Hisba Ta Sake Cafke Matasa 18 Ciki Har Da yan kasashen ketare

Daga Fauziyya Momin Haidar

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta turo wa hukumar hisbar wasu matasa 38, da aka kamo su a kasuwar Tumatir ta Kwanar Gafan,

Alfijir labarai ta rawaito a ci gaba da kai sumame da hukumar Hisba ta jihar Kano ke yi, a wuraren da ake zargin Maza da Mata na taru wa don aikata masha’a, a sassan jahar, ta samu nasarar kama matasa 18, a simamen ta mai ta ken, Operation Kauda Badala, don tsaftace jahar daga dukkan munanan aiyuka.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisba Dr. Mujahid Aminuddeen Abubakar shi ne ya tabbatar hakan ga jaridar Idongari, a daren Lahadi.

Dr. Mujahid ya ce, sun kamo maza 9 da kuma mata 9, a yakunan Zangon Dakata, Bakin River Bird Sabon Gari, Airport Road, Titin Asibitin Nasarawa, Alu Avenue, Titin Mumdubawa, Ahmadu Bello Way da kuma Hadejia Road.

Ya kara da cewa, cikin wadanda aka kama harda wasu da suka zo daga kasashen waje, domin yin bikin Birthday.

” Yanzu me za a yi da bikin Birthday ana fama da abinda za a ci, amma sai an hada maza da mata an yi bidi’a domin koyi ne da yahudawa”.

Haka zalika rundunar yan sandan jahar Kano, ta turo wa hukumar hisbar wasu matasa 38, da aka kamo su a kasuwar Tumatir ta Kwanar Gafan, wadanda mafi ya wansu suna dauke da juna biyu da kuma masu goyo da suka haifa a Kasuwar .

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *