Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar.
Bayanan hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka shafi aiwatar da tsare-tsaren sabunta tsarin aiki.
Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce an fitar da sunaye da hotunan jami’an da abin ya shafa domin ankarar da jama’a.
“A wani ɓangare na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a hukumar DSS, an sallami jami’ai 115. Don haka ana gargaɗin jama’a da su guji yin hulɗa da waɗannan mutanen da aka sallama daga aiki,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na tsaftace hukumar da tabbatar da ingantaccen aiki da gaskiya a tsakanin jami’anta da al’umma.


Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇