Hukumar NDLEA Ta Kama Dala Miliyan 20 Ta Jabu

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin dalar Amurka ke kara hawa da sauka a Nijeriya

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’an hukumar NDLEA wadda ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya sun ce sun kama dalar Amurka miliyan 20 ta jabu.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta yi kamen ne a kan hanyar Abaji zuwa Lokoja a cikin birnin Abuja babban birnin kasar.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya tabbatar da cewa an samu kudin na jabu a cikin wata mota wadda ta taso daga Legas zuwa Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa an kama direban motar mai suna Onyebuchi Nlededin mai shekara 53.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin dalar Amurka ke kara hawa da sauka a Nijeriya.

Hukumar ta NDLEA ta ce kwana guda kafin ta kama dalolin na bogi, sai da ta kama wani mutum mai suna Jude Ndubuisi mai shekara 52 da kilo 2.2 na kwayar methamphetamine a wani samame da jami’an hukumar suka kai a kauyen Kabusa da ke Abuja.

Hukumar ta ce tun da farko ta kama mutumin da take zargi da kilo 20.75 na tabar wiwi a ranar 7 ga watan Yulin 2022 inda kotu ta bayar da belinsa, a yayin haka ne aka soma kama shi kan zargin wani laifin.

Haka kuma hukumar ta NDLEA din ta kai wani samame a matattarar ‘yan shaye-shaye biyu a unguwannin Dei Dei da Tora-Bora da ke Abuja inda aka gano kilo 1.8 na rohypnol da kilo 1.2 na diazepam a ranar Laraba 16 ga watan Agusta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *