Ibtila’i! Ƴan Bindiga Sun Kashe Malamin Jami’ar FUDMA, Sun Tafi Da ‘Ya’yansa

FB IMG 1718099197879

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan wani malami a jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke jihar Katsina mai suna Dakta Tiri Gyan David,

Lamarin ya faru ne a Lowcost Yarima Quarters da misalin karfe 1:30 na dare a ranar Talata, 2 ga Yuli, 2024.

Alfijir labarai ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kashe malamin tare da sace ‘ya’yansa guda biyu. Malamin, mai suna Dakta Tiri Gyan David, shi ne Shugaban sashen tattalin arziƙi na noma, bunƙasawa da raya Karkara a jami’ar FUDMA.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun dira a Unguwar ne da manyan makamai tare da yin harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa harbe-harben da aka yi ya sa suka farka: “Mun shiga damuwa matuƙa, da misalin ƙarfe 1:35 na dare, sai muka ji ƙarar harbe-harbe ta ko’ina a Unguwar, daren ya kasance mana mai ban tsoro. Sai muka ji kuma an kashe wani malamin FUDMA, sannan an sace wasu daga cikinsu ‘ya’yansa”.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, Aliyu Sadeeq, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa.

Dakta Tiri Gyan David,
Dakta Tiri Gyan David,

Jaridar Daily Struggle
   
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Jaridar Daily Struggle
   
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *