Ibtila’i! Fasinjoji 85 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hatsarin Jirgin Sama 10, Sun Jikkata

Screenshot 20240510 113236 Facebook

Daga Aminu Bala Madobi

Wani jirgin sama samfurin 737 dauke da mutane 85 ya tsallake rijiya da baya a filin jiragen sama na Dakar, da ke kasar Senegal, inda ya raunata mutane 10, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Alfijir labarai ta rawaito mawakin kasar mai suna, Mali Cheick Siriman Sissoko wanda ya wallafa yadda lamarin ya auku a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa, “Jirgin da muke ciki kawai ya kama da wuta,” yana mai cewa kururuwar mutane ta cika cikin jirgin a lokacin da al’amarin ya faru.

Ministan Sufuri El Malick Ndiaye ya ce jirgin Air Senegal ya nufi Bamako babban birnin kasar Mali da ke makwabtaka da kasar da yammacin Laraba, dauke  da fasinjoji 79 sai kuma matukan jirgi biyu da ma’aikatansa guda hudu.

Wadanda suka jikkata dai suna karbar kulawar likitoci a asibiti yanzu haka, yayin da sauran kuma aka kai su otel domin su huta.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani kan musababbin faruwar hatsarin jirgin.

Cibiyar Safety Network mai bin diddigin hadurran jiragen sama, ta wallafa hotunan yadda jirgin ya kafe a cikin wani fili mai dauke da ciyawa a shafinta na X.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *