Ibtila’i: Mutane 17 Sun Mutu, 17 Sun Jikkata A Wasu Hadarin Hatsarin Mota

Alfijr ta rawaito akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a wurare daban-daban guda biyu a jihar Bauchi a ranar Litinin, 13 ga Maris, 2023.

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu a hatsarin na farko, hatsarin na biyu ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida.

Rahoton da ya fito daga ofishin RS12.11 Azare-Gamawa na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar, daya daga cikin hadarurrukan ya afku ne a kauyen Manaba dake kan hanyar Zaki zuwa Gamawa, wanda ya shafi mutane 25 a ranar Litinin.

Mutane 11 da suka hada da manya maza biyu da manya mata tara ne suka mutu a hatsarin yayin da mutane 13 da suka kunshi manya maza uku da mata manya 10 suka samu raunuka.

Hadarin daya tilo ya shafi wata farar motar bas Toyota Hummer mai lamba KTG 13XF ta kasuwanci da wani Haruna Yusuf a cikin tawagar Himma Express.

Hadarin na biyu ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da jikkata wasu hudu a matakai daban-daban.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *