Ibtila’i! Wasu mutane da dama sun mutu wasu sun jikkata yayin da wata Tirela ta yi haɗari a Kano

FB IMG 1739528254030

Ba a tabbatar da adadin mutanen da su ka rasa rayukansu ba, yayin da wasu su ka jikkata bayan da wata tirela ta fadi a kan gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro, cikin birnin jihar Kano.

An ce tirelar da ta yi hatsarin na kan hanyarta zuwa kudancin ƙasar nan.

Da ya ke tsokaci kan lamarin, wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Yahya Abubakar Sadiq, ya rubuta cewa: “A yanzu haka, a Hotoro NNPC, ƙarƙashin gadar daga Mariri zuwa Unguwa Uku, wata tirela ta kife, tana ɗauke da mutane da kayayyaki. Akalla fiye da mutane ashirin ne abin ya shafa; wasu sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka samu raunuka masu muni.”

Wani ganau, Shu’aibu Hamisu, ya ce tirelar ta rasa iko ne yayin da take tahowa daga hanyar Maiduguri tana ƙoƙarin bi ta cikin ƙarƙashin gadar don shiga hanyar ring road da ta haɗa zuwa babbar hanyar Zariya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa irin waɗannan haɗurra da suka shafi tireloli sun faru a wannan wurin a lokuta daban-daban a cikin shekarar da ta gabata.

Mota-motan da abin ya shafa galibi su ne tireloli masu ɗaukar dabbobi, kayan abinci da mutane daga yankin arewacin ƙasar zuwa kudanci.

Da Daily Trust ta tuntubi kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce suna ci gaba da tattara cikakken bayani kan lamarin.

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *