Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’unAllah Ya Yiwa Sarkin Damaturu Na Farko Rasuwa  A Saudiya Yana Da Shekaru 82

Screenshot 20240423 113109 Facebook

Ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, ya bar ’ya’ya da matarsa kamar yadda dan n uwansa Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana wa Aminiya.

Marigayi Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri an nada shi a matsayin Sarkin Damaturu a zamanin Marigayi gwamna Sanata Bukar Abba Ibrahim a watan Agusta 1993.

A cikin kankanin  lokaci da aka samu juyin mulkin soja sai gwamnatin soja ta tsige shi a watan Janairun 1995, kasa da shekaru biyu da hawansa karagar sarautar ta Damaturu.

Kafin zamansa sarki, Alhaji Biriri ya rike mukamai da dama, ciki har da kwamishinan kudi a shekarar 1984 a tsohuwar jihar Borno.

Ya kuma taka rawar gani wajen jagorantar musanya kudin da gwamnatin mulkin soja ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi a shekarar 1984.

Bugu da kari, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya taba rike mukamin Manajan Daraktan Hukumar samar da takardun kudi ta kasa.

Ya kuma rike Kwamishinan Hukumar kidaya ta kasa mai kula da Jiharsa ta Yobe da sauran mukamai.

Tunin dai aka yi jana’izarsa a Masallacin Harami da ke Makkaha kasar Saudiyya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *