Jami’an DSS Sun Cafke Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara A Kano

FB IMG 1719567489337

Jami’an Hukumar tsaro ta DSS a Kano sun kama ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya sace mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara. Yayin artabun guda daga cikin masu garkuwar ya mutu wani wanda ake zargi da kuma samun kudi har ₦26.5 miliyan.

Alfijir labarai ta ruwaito wani babban jami’i a hukumar DSS ya bayyana cewa, tawagar musamman ta DSS, bisa ga bayanan sirri masu inganci, sun kama wata tawaga ta ‘yan bindiga biyar a dajin Maƙarfi yayin da suke raba kuɗin fansa.

An kama ɗaya daga cikin su, Hamisu Tukur, da raunin harbin bindiga, yayin da aka kashe wani wanda ake zargi, Bature.

Lamarin sacewar ya faru ne makonni uku da suka gabata lokacin da wasu ‘yan bindiga suka shiga gidan Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar Rarara, a Kahutu, suka yi garkuwa da ita.

Ta samu ‘yancinta bayan ta shafe kwanaki 20 a hannun masu garkuwa.

Leadership Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *