Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Babban Jigo Na Jam’iyyar NNPP A Kano

Alfijr ta rawaito Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar Kano, Yusuf Imam wanda aka fi sani da Ogan Boye, ya shiga hannun jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Sahelian Times ta wallafa cewa an kama Ogan Boye ne da sanyin safiyar ranar Litinin a gidansa da ke cikin karamar hukumar Nasarrawa inda aka garzaya da shi hedikwatar rundunar da ke Bompai.

Duk da cewa ba a bayyana dalilin da ya sa aka kama Imam ba, amma akwai yiyuwar an tsare Imam dangane da yanayin dambarwar siyasar jihar Kano a kwanakin baya, inda aka samu takun saka tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta NNPP a sassa daban-daban na jihar.

Kwanakin baya kungiyoyin biyu sun yi arangama a wurare daban-daban a karamar hukumar Nasarrawa inda mataimakin gwamna kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Ogan Boye na NNPP duk suka fito.

Haka kuma an yi taho mu gama tsakanin magoya bayan jam’iyyun biyu a unguwar Charanci da ke karamar hukumar Gwale inda dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP, Alhaji Abba Kabir Yusuf da shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Abdullahi Abbas duk suka fito.

Abdullahi Abbas, a wajen gangamin yakin neman zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar kwanan nan a Gaya, ya bayyana cewa ba za a iya kayar da jam’iyyarsa ba, kuma tana shirin lashe zaben gwamna na shekara mai zuwa ta hanyar magudi ko damfara.

Sai dai shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Hon Umar Haruna Doguwa a lokacin da yake mayar da martani ga Abbas, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu a shirye take ta daidaita rigingimun da jam’iyya mai mulki ke yi domin samun nasara ta hanyar kuri’a.

Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar kan kamun Ogan Boye ya ci tura domin jami’in hulda da jama’a na hukumar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kasa samunsa a wayarsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *