Jam’iyyar NNPP ta yiwa Atiku Abubakar martani kan Kwankwaso

NNPP ba ta je kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu, don haka ba za ta yi shisshigi ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Jam’iyyar NNPP ta yi wa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar martani da cewa ya daina neman janyo dan takararta Sanata Rabiu Kwankwaso cikin shari’arsa ta kalubalantar zaben nasara Shugaba Tinubu a zabe.

A ranar Alhamis Atiku ya yi taron ’yan jarida inda ya bukaci dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, da kuma Kwankwaso wanda shi ne dan takarar NNPP, su hada kai da shi, wajen fallasa abin da ya kira asirin Tinubu.

Amma a martanin NNPP a wani taron ’yan jarida a Abuja, Sakaraten jam’iyyar na kasa kuma mukaddashin mataimakin shugaban jam’iyyar, Prince Nwaeze Onu, ya bayyana cewa NNPP ba ta je kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu, don haka ba za ta yi shisshigi ba.

Don haka Atiku da PDP su san inda dare yayi musu su yi ta kansu, su bar neman janyo NNPP cikin abin da bai shafe ta ba.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *