Jam’iyyar APC A Jihar Kano Ta Dakatar Da Waɗanda Suka Dakatar Da Ganduje.

FB IMG 1707908149590

Shugabancin Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas ya Dakatar da Shugabannin Jam’iyyar na Mazaɓar Ganduje, waɗanda suka dakatar da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje daga Jam’iyyar.

Alfijir Labarai ta rawaito Abbas ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sun ɗauki matakin ne biyo bayan rahoton sirri da suka samu akan yadda shugabannin suka yi wata ganawar sirri da ɓangaren Adawa.

A cewar Abdullahi Abbas, “Muna da Hujjoji masu ƙarfi na yadda waɗancan Shugabanni da muka kora suka yi taro da Muƙarraban Gwamnatin Kano.

Shima Shugaban Jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Inusa Dawanau ya shaidawa manema labarai cewar sun dakatar da dukkan waɗanda suke da hannu akan lamarin, a sakamakon kama su da da yunƙurin cin amanar Jam’iyyar ta hanyar yin taro da tsagin adawa.

Kwamitin ayyukan Jam’iyyar na jihar Kano ya ce Dakatarwar ta Watanni Shida ce domin a sami damar gudanar da bincike kan tarin Zarge-zargen da ake yi musu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *